24 Janairu 2022 - 20:14
​Burkina Faso : ECOWAS Ta Bukaci Sojoji Su Koma Barikinsu

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS, ta yi Allah wadai da abunda ta danganta da yunkurin juyin mulkin da ba za'a taba amincewa da shi ba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A wata sanarwa da ta fitar a shafinta na tuwita Ecowas, ta danganta halin da ake ciki tun ranar Lahadi a Burkina faso da babban laifi.

Sanarwar ta kuma bukaci sojoji su koma. barikinsu, su kuma baiwa shugaban kasar Marck Rock Christian Kabore, kariya da kular da ta dace.

Kungiyar ta kuma dora duk halin da shugaban zai iya shiga akan sojojin.

A Burkina faso dai ana cikin zaman dar dar tun bayan boren da sojoji sukayi a jiya inda hanzu haka bayanai ke cewa sojoji su na tsare da shugaba Kabore da kuma, wasu jami'an gwamnatinsa.

342/